ABNA24 : Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ‘’an samu ci gaba a tattaunawar da aka kwashe makonni biyu anayi, kuma an cimma ababe da dama.
Saidai a yanzu bangarorin da ke halartar tattaunawar zasu koma gida domin tuntuba game da wasu batutuwa da suka rage dake bukatar dogon nazari.
Muna fatan cimma fatan cimma matsaya a zagaye na gaba na tattaunawar a cewar Abbas Araqchin.
Batun dage wa Iran takunkuman da tsohuwar gwamatin Donald Trump na Amurka ya kakaba ma ta da kuma sake dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar ta 2015 na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye ajandar tattaunawar ta Vienna.
342/